Connect with us

Featured

Cutar Ƙyanda Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 153 a Najeriya – NCDC

Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Ƙasa (NCDC) ta bayyana cewa, an tabbatar da cewa mutane 19,213 sun kamu da cutar kyanda, daga cikin 26,866 da ake zargi da cutar a fadin kananan hukumomi 507 na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT). Hukumar ta ce zuwa watan Nuwamban 2025, cutar ta yi sanadin mutuwar mutum 153, kamar yadda ta bayyana a rahoton da ta fitar a Abuja ranar Talata, 24 ga Disamba, 2025.

Rahoton ya kuma nuna cewa, daga Janairu zuwa Nuwamba 2025, jihohin Borno, Zamfara, Yobe, Bauchi da Kebbi sun fi yawan wadanda ake zargin sun kamu da cutar, inda suka kai kashi 66.1% na dukkan adadin. Daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu, yara masu shekaru 9 zuwa watanni 59 ne suka fi yawa da kusan rabin adadin, yayin da aka ce kashi 77% ba su taba karbar rigakafin kyanda ba. NCDC ta kuma jaddada cewa cutar kyanda na yaduwa cikin sauki ta hanyar tari, atishawa ko kusantar mai dauke da ita, kuma tana iya ci gaba da yaduwa a iska ko kan abubuwa har na tsawon sa’o’i biyu.

Hukumar ta kara da cewa, kananan hukumomi 188 a jihohi 27 sun fuskanci barkewar kyanda a wannan lokaci, sai dai zuwa karshen Nuwamba 2025, LGA daya kacal – Eti-Osa a Jihar Legas ke da barkewar cutar da ke ci gaba. A wani mataki na dakile yaduwar cutar, Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da shirin rigakafin Kyanda–Rubella a ranar 6 ga Oktoba, wanda ake sa ran zai shafi kusan yara miliyan 106 a fadin kasar, a wani gagarumin shirin kiwon lafiya da ake cewa shi ne mafi girma a Afirka.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet