Featured
Tashin Farashin Tikitin Jirgin Sama Ba Shi Da Alaƙa da Batun Haraji – NCAA

Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta musanta iƙirarin cewa harajin gwamnati ne ya haddasa tashin farashin tikitin jiragen sama na cikin gida a watan Disamba, tana mai cewa babu alaƙa tsakanin haraji da hauhawar farashin.
Daraktan hulɗa da jama’a da kare haƙƙin masu amfani na NCAA, Michael Achimugu, ya bayyana a shafinsa na X a ranar Lahadi cewa hauhawar farashin ta samo asali ne daga yanayin kasuwa, musamman yawaitar buƙatar tafiya a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.
Ya ƙara da cewa irin wannan hauhawar farashi abu ne da ke faruwa duk shekara, ba a harkar jiragen sama kaɗai ba, tare da bayyana cewa ana sa ran farashin zai fara raguwa a watan Janairu, musamman bayan mako na biyu yayin da buƙatar tafiya ke raguwa.