Featured
Bankuna Za Su Fara Cire ₦50 Kan Duk Mu’amalar Da Ta Wuce ₦10,000 Daga Janairu 2026
Bankuna a Najeriya sun sanar da cewa za su fara cire Naira 50 a matsayin harajin banki kan duk kuɗin da aka tura ko aka cire da ya wuce Naira 10,000, daga ranar 1 ga Janairun 2026. Wannan mataki ya biyo bayan sabuwar dokar haraji da aka kafa, kamar yadda bankuna suka sanar wa kwastomominsu ta wasiƙu.
Sabon tsarin na nufin cewa duk wata mu’amala ta kuɗi da ta wuce Naira 10,000, ko ta shigo ko ta fita daga asusun banki, za a cire Naira 50 kai tsaye. Sai dai bankunan sun bayyana cewa harajin ba zai shafi albashi da ke shiga asusun mutum ba, haka nan ba zai shafi kuɗin da aka tura tsakanin asusu na banki iri ɗaya ba.
Bankunan sun ƙara da cewa a baya wanda aka tura wa kuɗi ne kaɗai ake cirewa wannan haraji, amma yanzu tsarin ya shafi mai tura kuɗin ma. Sun kuma jaddada cewa harajin ya bambanta da sauran cajin banki da aka saba, kuma za a nuna wa kwastoma a sarari a lokacin da yake aiwatar da mu’amala.
