Featured
Gwamnatin Gombe Za Ta Kashe Naira Miliyan 665 Wajen Biyawa Ɗalibai Kuɗin SSCE
Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da kashe N665 miliyan don biyan kudin jarabawar Senior Secondary School Certificate Examination (SSCE) ga dalibai 23,873 a jihar. Hakan ya fito fili ne daga kwamishinan ilimi, Aishatu Maigari, yayin taron manema labarai a gidan Gwamnatin Jihar, bayan zaman Hukumar Zartarwa karkashin jagorancin Gwamna Inuwa Yahaya.
Maigari ta bayyana cewa daliban sun cancanci tallafin ne bayan an gudanar da jarabawa ta gwaji ga ‘yan takara 26,857, inda 23,873, wato kashi 88 cikin 100, suka samu maki 50 ko fiye. Daga cikin su, 21,909 za su yi jarabawar WAEC, 1,431 na NABTEB, yayin da 297 za a gabatar da su don NBAIS. Haka zalika, an hada da ɗalibai 183 wadanda ‘ba daga jihar ba’ da 53 masu bukatun musamman.
An bayyana cewa za a raba biyan kudin ne a tsakanin gwamnati da kananan hukumomi 11, bisa tsarin kashi 60-40. Wannan mataki na daga cikin shirin Gwamna Yahaya na kawar da matsalolin kudi wajen ilimi, inganta sakamakon karatu, da sanya Gombe a matsayin cibiyar ilimi mai tasiri a Arewa-Maso-Gabashin Najeriya.
