Featured
Mun Dakatar Da Kama Motoci Masu Gilashi Mai Duhu – Rundunar Ƴansanda

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta dakatar da aiwatar da dokar izinin gilashin mota mai duhu (tinted) a faɗin ƙasar, biyo bayan umarnin wucin-gadi da wata kotu ta bayar. Rundunar ta bayyana cewa kotun ta hana ta ci gaba da aiwatar da dokar har sai an kammala sauraron shari’ar ko an janye umarnin.
Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin, ya ce an bai wa ‘yan sanda umarnin kotu tun ranar 17 ga Disamba 2025 a shari’a mai lamba HOR/FHR/M/31/2025. Ya ƙara da cewa rundunar ta shiga shari’ar tare da shigar da ƙorafe-ƙorafe, kuma kotu ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 20 ga Janairu 2026.
Rundunar ta jaddada cewa tana bin doka da mutunta ikon kotu, inda ta tabbatar da cewa an dakatar da aiwatar da dokar izinin gilashin mota a duk faɗin ƙasa. Sai dai ta ce za ta ci gaba da amfani da hanyoyin tsaro na halal da bayanan sirri domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.