Featured
Kotu Ta Bayar Da Umarni Tsare Direban Anthony Joshua a Gidan Gyaran Hali

Wata kotu a jihar Ogun ta ajiye direban motar Lexus SUV da ya ɗauki fitaccen ɗan damben duniya Anthony Joshua, Kayode Adeniyi mai shekaru 46, a gidan yari bisa hatsarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar abokan Anthony Joshua guda biyu. Hatsarin ya faru ne ranar Litinin da misalin ƙarfe 11 na safe, lokacin da motar ta buge wata babbar mota da aka ajiye a bakin hanya.
’Yan sandan Ogun sun bayyana cewa mutanen da suka rasu su ne Ayodele Kelvin Olu, ɗan Najeriya-Birtaniya mai shekaru 36, da Gami Sina, ɗan ƙasar Birtaniya mai shekaru 36. An gurfanar da direban a gaban kotu da laifuka huɗu da suka haɗa da tuƙin ganganci wanda ya haddasa mutuwa, tuƙi ba tare da kulawa ba, da kuma tuƙi ba tare da lasisin ƙasa ba.
Kotun ta bayar da beli na naira miliyan biyar tare da masu tsaya masa biyu, amma aka ajiye shi a gidan yari har sai ya cika sharuɗɗan belin. An ɗage shari’ar zuwa ranar 20 ga Janairu, 2026, yayin da gwamnatocin Lagos da Ogun suka tabbatar da sallamar Anthony Joshua daga asibiti bayan hatsarin.