Featured
An Sanya Kalmar ‘Amala’ Acikin Kudin Kalmomi Na Oxford

Kundin Oxford English Dictionary (OED) ya ƙara wasu kalmomi da suka samo asali daga Najeriya a sabuwar sabuntawar sa ta Disambar 2025, lamarin da ke nuna ƙaruwa da tasirin harshen Najeriya, al’adu da abinci a duniya.
Daga cikin kalmomin da aka amince da su akwai “nyash”, “mammy market”, “amala”, “moi moi”, “abeg”, “biko” da “Ghana Must Go”, tare da “Afrobeats” wadda aka bayyana a matsayin salon waka mai haɗa kiɗan Yammacin Afirka da jazz, soul da funk.
Oxford ya bayyana cewa an samo waɗannan kalmomi ne daga amfani da Ingilishi na Yammacin Afirka, inda ya jaddada cewa Ingilishi na Najeriya, Pidgin da salon magana na titi na ci gaba da yin tasiri a ƙamus ɗin duniya, kamar yadda aka taba ƙara kalmomi irinsu japa, 419 da eba a baya.