Featured
2027: Kwankwaso Ba Zai Sake Takara a Jam’iyyarmu Ba – NNPP
Sakataren jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na kasa, Ogini Olaposi, ya bayyana cewa Rabiu Musa Kwankwaso ba zai samu damar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar a zaben 2027 ba. Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Lagos.
Olaposi ya ce tikitin shugaban kasa na NNPP a 2027 zai kasance a bude ga mambobin jam’iyyar na gaskiya kadai, ba kamar 2023 ba da aka bai wa Kwankwaso shi kadai. Ya kara da cewa sabanin da ya barke tsakanin NNPP da kungiyar Kwankwasiyya, da kuma karewar yarjejeniyar hadin gwiwa da suka kulla a 2022, ne ya haddasa wannan matsaya.
A cewarsa, an kori Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigai sakamakon ayyukan cin amanar jam’iyya bayan zaben 2023, kuma ba a janye hukuncin ba. Olaposi ya ce NNPP na bude kofarta ga sababbin masu neman takara da hadin gwiwa da jam’iyyun da ke da akida iri daya, yana mai jaddada cewa kwamitin gudanarwa na kasa ne kadai ke da ikon yanke hukuncin kawance a 2027.
