Featured
NDLEA Ta Cafke Dattijo Mai Shekara 80 Da Kilo 5.7 Na Wiwi
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta sanar da kama mutane da kwace kwayoyi a jihohi da dama ciki har da Akwa Ibom, Oyo, Edo, Niger, Taraba da Adamawa, a wani bangare na ci gaba da ayyukanta na dakile fataucin miyagun kwayoyi.
Daga cikin wadanda aka kama akwai Jeremiah Isaiah Nkanta mai shekaru 80, tsohon fursuna, wanda aka cafke a gidansa da ke Mmanta-Abak a karamar hukumar Abak ta Akwa Ibom, dauke da kilo 5.7 na skunk. An ce an taba yanke masa hukunci a Disamba 2022 kan fataucin kwayoyi, inda ya yi zaman gidan yari na tsawon shekaru biyu.
A wani samame daban a Akwa Ibom, an kama dan kasuwa Ani Onyebuchi Romans mai shekaru 37 da ke safarar tramadol kilo 5.3 cikin kayan kwalliya, yayin da a sauran jihohi aka cafke mutane tare da kwace wiwi, tramadol da wasu kwayoyi. Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya yabawa jami’an hukumar bisa jajircewarsu wajen rage yaduwa da amfani da miyagun kwayoyi a fadin kasar.
