Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan N12.78 Domin Shirin Ƙidayar Jama’a
Gwamnatin Tarayya ta ware kudin Naira biliyan 12.78 ga Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) a cikin daftarin kasafin kudin 2026. Kudaden sun shafi ayyukan kidayar jama’a, gina ofisoshin dindindin da kuma sayen motocin aiki.
Bisa bayanan da ke cikin kudirin kasafin, an ware N770m domin aikin kidayar jama’a da gidaje, yayin da N8.4bn aka tanada domin gina ofisoshin NPC. Haka kuma, N2.8bn za a kashe wajen sayen motocin aiki ga kwamishinonin hukumar.
Kasafin ya kuma tanadi kudade domin bayanan jama’a, wayar da kai kan kidaya, bincike, rajistar haihuwa da mutuwa, da sauran ayyukan fasaha. An gudanar da kidaya ta ƙarshe a shekarar 2006, kuma har yanzu ana fuskantar kalubale wajen shirya sabon kidayar a fadin kasar.
