Featured
Kisan Gilla a Chiranchi: Gwamnatin Kano Za Ta Jagoranci Gurfanar da Masu Laifi
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta jagoranci shigar da ƙara kan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke birnin Kano. Gwamnatin ta bayyana lamarin a matsayin mummunan aiki na rashin tausayi da ya girgiza al’ummar jihar baki ɗaya.
A cikin sanarwar da Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya fitar, ya ce bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, gwamnati ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da al’ummar Kano. Ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta yi watsi da iyalan da abin ya shafa ba a wannan mawuyacin lokaci.
Gwamnatin ta yaba wa rundunar ’yan sandan jihar bisa gaggawar kama manyan waɗanda ake zargi, tare da jaddada cewa za a gudanar da shari’ar cikin gaggawa da ƙwarewa. Sanarwar ta ce Ofishin Babban Lauyan Jihar zai kafa tawagar lauyoyi ta musamman domin tabbatar da ganin an yi adalci.
