Featured
Ƴansanda sun gurfanar da Sheikh Makwarari a gaban Kotu

’Yan sanda sun gurfanar da Sheikh Ibrahim Isa Makwarari a gaban Kotun Majistri ta 53 da ke Normansland a Kano, bisa zargin harƙallar filayen gwamnati da na al’umma. An gudanar da zaman kotun ne ranar Talata, 20 ga Janairu 2026, karkashin jagorancin Mai Shari’a Mustapha Sa’ad Datti.
A zaman kotun, lauyan wanda ake zargi ya bayyana cewa ba su shirya gabatar da shi ba, inda ya sanar da kotu cewa akwai wata shari’a makamanciya da ke gaban wata babbar kotu. Hakan ya sa lauyoyin suka nemi kotu ta ba su lokaci kafin a ci gaba da shari’ar.
Mai gabatar da kara, Barista Nura, ya ce tun ranar 18 ga Nuwamba aka shigar da shari’ar, amma daga bisani aka mayar da takardun zuwa ma’aikatar shari’a domin neman shawara. Bayan sauraron ɓangarorin biyu, kotu ta ɗage shari’ar zuwa Laraba, 21 ga Janairu 2026, tare da bayar da belin wanda ake zargi bisa wasu sharaɗi.