Featured
Barau Ya Raba Tallafin Karatu Ga Dalibai 4,183 a Kano

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya raba tallafin karatu ga dalibai 4,183 daga Yankin Kano ta Arewa da ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Technical) da ke Bichi, Jihar Kano. Tallafin ya shafi dalibai maza da mata masu karatun NCE da Digiri.
Daliban NCE sun samu N20,000 kowanne, yayin da daliban Digiri suka karɓi N50,000 kowanne. An gudanar da rabon tallafin ne a ranar Laraba a dakin taro na kwalejin, ta hannun wata tawaga da Babban Ma’aikacin Ofishin Sanatan ke jagoranta, Farfesa Muhammad Abdallah.
An bayyana cewa tallafin na daga cikin ci gaba da zuba jari da Sanata Barau ke yi a fannin ilimi a Kano ta Arewa, tare da aiwatar da ayyuka daban-daban a kwalejin. Shugabannin makarantar sun yaba da tallafin, suna masu cewa ya kawo gagarumar gudunmawa ga rayuwar dalibai da inganta harkokin ilimi.