Featured
Za Mu Ɗauki Mataki Kan Duk Masoyin Gwamna da Ya Ci Zarafin Kwankwaso – Gwamnatin Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta ja kunnen magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da su guji yin kalaman tayar da hankali ko cin zarafin Madugun tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ta ce duk wanda ya aikata hakan zai fuskanci matakin ladabtarwa.
Gargadin ya fito ne daga Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Fadar Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, yayin rabon babura ga ‘yan jam’iyya a filin Open Space Theatre da ke Fadar Gwamnati, a gaban Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Bature ya ce gwamnati ba za ta lamunci rashin ɗa’a ko raini ga Kwankwaso ba, yana mai jaddada buƙatar magoya bayan gwamnan su nuna haƙuri a siyasa, tare da gujewa kai hare-haren kalamai, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauyen siyasa a jihar Kano.
