Featured
Al’umma Sun Shiga Fargaba Bayan Jiyo Ƙarar Harbe-harbe a Kusa da Filin Jirgin Sama na Niamey

A daren jiya ne aka ji ƙarar harbe-harbe da fashe-fashe a kusa da filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Diori Hamani da ke Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar. Shaidun gani da ido sun ce an fara jin ƙarar ne da misalin ƙarfe 12 na dare, kuma lamarin ya ɗauki wani lokaci ana yi.
Kafar LSI Africa ta ruwaito cewa wasu faye-fayen bidiyo da suka karaɗe kafofin sada zumunta sun nuna haske yana tashi daga yankin da ake jin harbe-harben. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin Nijar ba su fitar da wata sanarwa ba kan ainihin abin da ya faru, ko kuma ko an samu asarar rayuka da dukiya.
Duk da haka, akwai rahotannin da ba a tabbatar ba da ke zargin yiwuwar mayaƙa masu iƙirarin jihadi ne suka yi yunƙurin kai hari a filin jirgin. Wasu kuma na hasashen cewa wata matsala ce ta cikin gida da ka iya alaƙa da boren sojoji, a yayin da Nijar ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro tun bayan juyin mulkin Yulin 2023.