Featured
Rikicin Masarauta Ya Kusa Zuwa Ƙarshe – Gwamnatin Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar wa al’ummar jihar cewa rikicin sarautar Kano da ya daɗe yana gudana zai zo karshe nan ba da jimawa ba. Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin ganawa da manema labarai a Kano.
Waiya ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ɗauki matakai masu muhimmanci domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya jaddada cewa gwamnati na bin hanyar tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki, tare da mutunta doka, sarakunan gargajiya da muradun jama’ar Kano.
Ya tunatar da cewa an dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 a watan Mayun 2024 bayan cire Aminu Ado Bayero, sakamakon soke dokar masarautu ta 2019. Kwamishinan ya kuma ce gwamnati na mai da hankali kan mulki, haɗin kai da ci gaba, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu yayin da ake ƙoƙarin warware dukkan batutuwan da suka rage.
