Featured
Ukraine Ta Karɓi Gawar Sojoji 1,000 Daga Rasha

Gwamnatin Ukraine ta bayyana cewa ta karɓi gawarwakin mutane 1,000 daga Rasha, waɗanda Moscow ta ce sojojin Ukraine ne da suka mutu a fagen fama. Hakan ya faru ne a ranar Alhamis, kamar yadda cibiyar kula da fursunonin yaƙi ta Ukraine ta sanar.
Musayar fursunonin yaƙi da gawarwakin sojoji na ɗaya daga cikin kaɗan daga cikin hanyoyin haɗin kai da suka rage tsakanin Kyiv da Moscow tun bayan da Rasha ta ƙaddamar da mamaya kan Ukraine a watan Fabrairun 2022. Rasha ta tabbatar da musayar, inda ta ce ita ma ta karɓi gawar sojojinta 38.
Wani jami’in Kremlin, Vladimir Medinsky, ya ce an cimma wannan musayar ne bisa yarjejeniyar da wakilan ƙasashen biyu suka kulla a birnin Istanbul a shekarar da ta gabata. Duk da asarar rayuka masu yawa a ɓangarorin biyu, babu ɗayansu da ke fitar da cikakken bayani kan adadin mutanen da suka mutu a yaƙin.