Featured
Matasa Sun Kashe Barawon Waya Tare da Ƙona Gawarsa a Ɗorayi

Rahotanni daga unguwar Dorayi da ke jihar Kano na nuna cewa wasu fusatattun matasa sun kama wani da ake zargi da fashin waya, inda suka yi masa dukan kawo wuƙa kafin daga bisani ya rasu.
Shaidun gani da ido sun ce wanda ake zargin ya yi wa wata matashiya fashin waya, inda ake zargin ya caka mata almakashi a kirji yayin da take ƙoƙarin kare kanta.
Bayan faruwar lamarin, matasan sun kone gawar wanda ake zargin, sai dai zuwa yanzu rundunar ƴansanda ta jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.