Featured
An Kashe Jami’anmu Sama da 100 a 2025 – FRSC

Hukumar kiyaye haɗurra ta Najeriya (FRSC) ta ce jami’anta fiye da 100 sun rasa rayukansu yayin da suke bakin aiki a shekarar 2025. Hukumar ta danganta yawaitar mutuwar da hatsarin ababen hawa da direbobi ke haddasawa.
Shugaban FRSC, Shehu Mohammed, ya shaida wa BBC cewa kusan jami’ai 127 ne aka rasa, inda yawancinsu direbobi suka buge su suna kan aiki. Ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda ake buge jami’an ko da suna tsaye a gefen hanya.
Sakamakon haka, FRSC ta fara kira ga gwamnatin tarayya da ta ba jami’anta damar riƙe makamai domin kare kansu. Shugaban hukumar ya ce idan aka amince, horo mai tsauri zai zama abu na farko domin tabbatar da bin doka da kare haƙƙin ɗan Adam.