Connect with us

Addini

Takunkumin Amurka: APC da NNPP Sun Mara wa Kwankwaso Baya

Jam’iyyun APC da NNPP sun yi watsi da ƙudirin wasu ’yan majalisar Amurka na sanya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ƙungiyoyin Miyetti Allah cikin takunkumi kan zargin take ’yancin addini.

Ƙudirin mai taken Nigeria Religious Freedom and Accountability Act of 2026 ya tanadi hana biza da daskarar da kadarori ƙarƙashin dokar Global Magnitsky.

APC ta ce zargi kaɗai bai isa a tauye haƙƙin motsi ba tare da cikakken sauraro da shari’a ba.

NNPP kuma ta bayyana matakin a matsayin baƙar magana, tana mai cewa tarihin Kwankwaso bai nuna alaƙa da tsattsauran ra’ayi ba, tare da kare matsayinsa kan aiwatar da Shari’a a Kano.

Ƙudirin ya yi nuni da yawaitar hare-haren addini a Najeriya, tare da kiran a sanya takunkumi kan waɗanda ake zargi da hannu.

Sai dai Miyetti Allah ta musanta zargin, tana mai cewa ƙungiya ce ta halal wadda ba ta da alaƙa da ta’addanci, tare da roƙon gwamnatin Najeriya ta shiga tsakani ta fuskar diflomasiyya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet