Featured
Ƙungiyar Rajin Kare Hakkin Ɗan Adam ta Duniya Ta Yi Allah Wadai da Cin Zarafin Ɗan Jarida A Kano

Wata Ƙungiya mai rajin kare hakkin ɗan Adam ta duniya reshen Najeriya, (Global for Human Rights Network Nigeria), ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan cin zarafin da aka yi wa ɗan jarida Abdulbaki Ali Ahmed Sharifai da ake zargin wani jami’in gwamnatin Jihar Kano, Auwal Sani Rogo (SSR), ya aikata a yayin wani taro na gasar kamun kifi na Argungu.
“Wannan abu ba wai cin mutuncin mutum ɗaya ba ne kawai, hari ne kai tsaye ga ’yancin aikin jarida da ’yancin faɗin albarkacin baki, da dimokuraɗiyya baki ɗaya.” Kamar yadda
Abin takaici, lamarin ya faru a gaban manyan jami’an gwamnati, amma har yanzu babu wata hukunci ko neman afuwa daga wanda ake zargi ko gwamnatin Jihar Kano.
Wannan shiru yana nuna rashin mutunta dokoki da kuma ƙoƙarin danne ’yan jarida.
Ƙungiyar ta ne mi gwamnatin Jihar Kano wa’adin sa’o’i 24 kacal ta dau matakin ladabtarwa kan wanda ake zargi.
Bayar da hakuri a hukumance ga ɗan jaridar tabbatar da kariya ga ’yan jarida a jihar idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, za mu garzaya kotu domin neman cikakken hakkinsa tare da ɗaukar dukkan matakan doka da suka dace.
Muna kira ga kwamashina Yansanda jahar Kano da Yakama ya gudanarda bincike sannan a gabatar da shi a gaban kutu, muna da majiya mai ƙarfi kan an shigar da korafi gaban kwamashina Yansanda jahar Kano amma har ya zuwa gaiyata da aka yi masa saboda kan a tsaye akan doka.
Wannan ba shi ne karo na farko ba, kwanan nan ma an samu cin zarafin ɗan jarida Aminu Halilu Tudunwada. Wannan yana nuna cewa cin zarafin ’yan jarida a Jihar Kano yana ƙara kamari, abin da ba za mu lamunta ba.
Muna kira ga Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da Kungiyoyin ’yan jarida da Lauyoyi da masu rajin dimokuraɗiyya da al’umma baki ɗaya da su tashi tsaye domin kare martabar aikin jarida kafin a mayar da shi abin tsoro.
’Yancin Jarida ba laifi ba ne ginshiƙi ne na adalci da gaskiya.
Duk wanda ya ci zarafin ɗan jarida, ya ci zarafin al’umma ne baki ɗaya.