Featured
Tinubu Zai Rantsar da Sabon Sufeto Janar Na Ƴansanda a Ranar Laraba

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai rantsar da Olatunji Disu a matsayin cikakken Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya ranar Laraba, 4 ga Maris 2026. Wannan na zuwa ne bayan Majalisar ’Yan Sanda ta ƙasa ta amince da naɗinsa a wani taro da aka gudanar a Abuja.
Naɗin Disu ya biyo bayan murabus ɗin tsohon IGP, Kayode Egbetokun, makon da ya gabata. Gwamnoni da manyan jami’an gwamnati sun yaba da ƙwarewarsa, musamman rawar da ya taka a Legas da kuma a Babban Birnin Tarayya wajen yaƙi da laifuka.
Disu mai shekaru 59 ya shiga aikin ’yan sanda tun 1992, inda ya riƙe muƙamai daban-daban har zuwa Mataimakin Sufeto Janar. Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ƙwarewarsa da iliminsa za su taimaka wajen inganta tsaro da aikin ’yan sanda a ƙasar.