Connect with us

Featured

2027: Ministocin Tinubu Huɗu Na Shirin Yin Murabus Daga Kujerunsu

Wasu sabbin lissafin siyasa gabanin zaben 2027 na iya haifar da sauye-sauye a majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu, yayin da ake zargin akalla ministoci hudu na shirin yin murabus domin tsayawa takarar mukaman siyasa a jihohinsu. Rahotanni sun nuna cewa wadanda ake ambata sun hada da Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu; Ministan Lafiya da Jin Dadin Jama’a, Muhammad Pate; Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar; da Karamin Ministan Kwadago, Nkeiruka Onyejeocha.

Bincike ya nuna cewa wasu daga cikinsu na shirin tsayawa takarar gwamna a jihohinsu, musamman a jihohin da gwamnoninsu za su kammala wa’adin mulki biyu a shekarar 2027. Dokar zabe ta shekarar 2026 ta tanadi cewa duk wanda ke rike da mukamin gwamnati dole ne ya yi murabus kafin ya shiga zaben fidda gwani na jam’iyyarsa.

Rahotanni sun kuma nuna cewa Adelabu na shirin sake tsayawa takarar gwamnan jihar Oyo, yayin da ake zargin Muhammad Pate da Yusuf Tuggar na duba yiwuwar tsayawa takarar gwamnan jihar Bauchi. Ita ma Onyejeocha ana zargin na shirin komawa majalisar wakilai, yayin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta gargadi jama’a da kada su yarda da jita-jitar cewa ta sanya ranar 26 ga Maris a matsayin wa’adin yin murabus ga masu son tsayawa takara.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet