Featured
Tambuwal Ya Fice Daga PDP, Ya Koma Jam’iyyar ADC
Sanatan da ke wakiltar Sokoto ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi murabus daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da sauya sheƙa zuwa African Democratic Congress (ADC), yana mai danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar.
A wata wasiƙar murabus da ya rubuta ranar 11 ga Maris 2026 zuwa ga shugaban PDP na mazabarsa a Tambuwal/Shinfiri da ke ƙaramar hukumar Tambuwal, Tambuwal ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon tunani da kuma shawarwari da abokan siyasarsa da magoya bayansa.
Ya ce duk da ficewarsa daga PDP, yana godiya ga damar da jam’iyyar ta ba shi wajen yi wa ƙasa hidima a matsayin kakakin majalisar wakilai da kuma gwamnan jihar Sokoto, ya ƙara da cewa ya koma ADC ne domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da samar da wata madadin jam’iyyar siyasa mai inganci.
