Featured
Jami’an Tsaro Sun Sake Kama Nasir El-Rufai Bayan Fitowarsa Daga Kotu

Rahotanni daga iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun bayyana cewa jami’an tsaro sun sake kamo shi jim kaɗan bayan fitowarsa daga kotu a yau, Talata. Wannan lamari ya jefa iyalansa da magoya bayansa cikin damuwa.
Majiyar ta ce an kama shi ne bayan kammala sauraron buƙatar belinsa, inda ake sa ran za a kai shi Abuja. Har yanzu ba a bayyana cikakken dalilin sake kamen nasa ba, amma ana danganta shi da binciken da hukumomi ke yi a kansa.
Sai dai hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma game da wannan lamari ba, lamarin da ke ci gaba da jawo tambayoyi a tsakanin jama’a.