Featured
Na Yi Iyakar Ƙoƙarina a Lokacin da Nake Shugaban Ƙasa – Goodluck Jonathan

Tsohon Shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Jonathan, ya kare gwamnatinsa yana mai cewa ya yi iya kokarinsa lokacin da yake kan mulki, bayan sukar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi masa a wata hira da ya gabatar.
Atiku ya bayyana Jonathan a matsayin wanda bai da kwarewa, yana cewa hakan ya janyo kura-kurai a mulkinsa, amma Jonathan ya ce babu wani shugaba da ba ya yin kuskure.
Jonathan ya kuma nuna nasarorin diflomasiyya da Najeriya ta samu a zamaninsa, ciki har da shiga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sau biyu, yana mai jaddada cewa zaman lafiyar siyasa shi ne ginshikin ci gaban tattalin arziki a kasashen Yammacin Afirka.