Featured
Ƴan Najeriya Ba Su Iya Turanci Ba – Shugaban Ƙasar Kenya

Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya kare tsarin ilimin ƙasarsa tare da cewa suna da ƙwarewa sosai a harshen Turanci, inda ya soki yadda ‘yan Najeriya ke magana da Turanci. Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ‘yan Kenya mazauna Italiya a wani bidiyo da ya bazu ranar Alhamis, 24 ga Afrilu, 2026.
Ruto ya ce Turancin Kenya na daga cikin mafi inganci a duniya, yana mai cewa sau da yawa ba ya fahimtar abin da ‘yan Najeriya ke faɗi sai an fassara masa. Sai dai wasu sun danganta kalamansa da wani furuci na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya ce ‘yan Najeriya sun fi wasu ƙasashen Afirka rayuwa mai kyau duk da matsin tattalin arziki.
Wannan musayar kalamai ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka soki salon kwatancen. Wasu sun ce harshe ba ma’auni ba ne na ci gaba, yayin da wasu suka mayar da martani ga kalaman Ruto, suna mai cewa bai kamata a raina al’adu da harsunan wasu ƙasashe ba.