Featured
Buba Galadima Ya Bukaci Atiku Ya Koma NDC

Jigo a jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Buba Galadima, ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ya shiga jam’iyyar, yana mai gargadin cewa zai iya ɗaukar alhakin gazawar haɗa kan ‘yan adawa kafin zaɓen 2027.
Galadima ya bayyana cewa nasarar haɗa kawancen ‘yan adawa ya dogara ne da yadda manyan ‘yan siyasa za su haɗu a ƙarƙashin NDC. Ya ce haɗin kai ne kaɗai zai iya ba su damar ƙalubalantar gwamnati, yana mai jaddada cewa yawancin jiga-jigan ‘yan adawa sun fara karkata zuwa jam’iyyar.
Sai dai ɓangaren Atiku ya musanta batun sauya sheƙa, inda mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya ce babu wata tattaunawa kan komawarsa NDC. Rahotonnin Kakaki24 ya kuma nuna cewa rabuwar kan ‘yan adawa a zaɓen 2023 ta taimaka wajen samun nasarar shugaba Bola Ahmed Tinubu.