Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano Ta Ba Wa Makarantu Hutu Domin Bukukuwan Babbar Sallah

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da hutun Babbar Sallah ga dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na ma’aikatar, Musbahu Aminu Yakasai, ya sanya hannu a ranar Laraba.

Sanarwar ta bayyana cewa daliban makarantun kwana za su tafi hutu daga ranar Asabar 23 ga watan Mayun 2026, sannan su koma makaranta ranar Lahadi 31 ga watan Mayun 2026. Ita kuwa bangaren makarantun yini, za su fara hutun ne daga Juma’a 22 ga watan Mayun 2026, tare da komawa makaranta ranar Litinin 1 ga watan Yunin 2026.

Ma’aikatar ta bukaci iyaye da masu kula da dalibai su tabbatar sun dauki yaransu a ranar rufe makaranta tare da mayar da su a kan lokaci bayan hutun. Haka kuma, Kwamishinan Ilimi na jihar, Gwani Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda, ya taya dalibai, malamai da iyaye murnar Babbar Sallah cikin zaman lafiya da farin ciki.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet