Addini
An Fara Gudanar da Ibadar Aikin Hajji Na 2026

A yau Litinin 25 ga Mayu, 2025 wanda ya yi dai dai da 08 ga Zul-Hijjah, 1447 Alummar musulmai ke fara gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 a ƙasar Saudi Arabia, duk da rikicin da ke cigaba da faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya sakamakon yaƙin da ya shafi Iran da sauran ƙasashe.
Hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa sama da mahajjata miliyan ɗaya da rabi daga ƙasashen waje ne suka isa ƙasar domin gudanar da ibadar bana, adadin da ya fi na shekarar da ta gabata duk da rikice-rikicen tsaro da ake fama da su a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa Saudiyya ta fuskanci wasu hare-hare tun bayan ɓarkewar rikicin tsakanin Iran da United States da kuma Israel, lamarin da ya sa ma’aikatar tsaron Saudiyya ta fitar da bidiyo domin nuna na’urorin kariyar sararin samaniya da aka girke a kewayen birnin Mecca don kwantar da hankulan mahajjata.