Featured
Majalisa Ta Sha Alwashin Gaggauta Gyara Kundin Tsarin Mulki Domin Kafa Ƴansandan Jihohi

Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana aniyarta na gaggauta aiwatar da matakan gyaran kundin tsarin mulki domin kafa rundunar ’yan sandan jihohi, a ƙoƙarin daƙile matsalolin tsaro, garkuwa da mutane da hare-haren ’yan bindiga da ke ƙaruwa a sassan ƙasar.
Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Harkokin Jama’a na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya ce majalisar ta shirya fara dukkan matakan doka da suka dace ba tare da bata lokaci ba, domin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wannan mataki na zuwa ne bayan sabbin kiraye-kirayen kafa ’yan sandan jihohi sakamakon tabarbarewar tsaro da kuma sace ɗalibai da malamai a Jihar Oyo. Kakaki24 ta rawaito cewa kudirin zai buƙaci amincewar Majalisar Tarayya da kuma akalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi kafin ya zama doka.