Featured
Ƴansanda Sun Kama Ƴan Daba da Dilolin Ƙwaya 345 a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da kama mutane 345 da ake zargi da aikata daba da safarar miyagun ƙwayoyi a wani samame da ta gudanar a faɗin jihar. Kwamishinan ’Yan Sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Bompai.
Ya ce an gudanar da aikin ne tsakanin ranar 5 zuwa 7 ga Yuni a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, inda aka kai farmaki wuraren da ake zargin masu aikata laifuka da masu safarar miyagun ƙwayoyi ke amfani da su. Daga cikin waɗanda aka kama, mutum 187 an cafke su ne a wannan sabon samamen kwanaki uku.
Rundunar ta kuma ƙwace makamai masu haɗari 270 da suka haɗa da wuƙaƙe, adduna da kulake, tare da miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da tabar wiwi, ƙwayoyin Exol da wani haɗin maye da aka fi sani da “Suck and Die”. Bakori ya ce za a gurfanar da duk wanda bincike ya tabbatar da laifinsa, yayin da Kakaki24 ke ruwaito cewa rundunar ta yi alƙawarin ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka a jihar.