Featured
Wasu Masu Neman Takarar Gwamna Sun Kashe Naira Biliyan 30 a Zuɓukan Fidda-gwani – EFCC

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa wasu masu neman takarar gwamna a Najeriya sun kashe tsakanin naira biliyan 20 zuwa 30 wajen samun nasara a zaɓukan fidda gwani. Ya ce wannan ɗabi’a na barazana ga dimokuraɗiyya tare da ƙara haifar da cin hanci a gwamnati.
Da yake jawabi a Jami’ar Ilorin ranar Laraba, Olukoyede ya ce yawan kuɗaɗen da ake kashewa a zaɓe na sa waɗanda suka ci zaɓe su riƙa karkatar da kuɗaɗen gwamnati domin dawo da abin da suka kashe. Ya kuma jaddada cewa EFCC za ta ci gaba da yaƙi da sayen ƙuri’u da sauran laifukan zaɓe.
Shugaban EFCC ya ƙara da cewa hukumar ta kama tare da gurfanar da mutane da dama kan laifukan sayen ƙuri’u a sassan ƙasar nan. Ya kuma bayyana shirin amfani da jiragen sa ido marasa matuƙa da sauran fasahohi wajen sa ido a zaɓukan 2027, tare da kira ga jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki su tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe cikin lumana. Kakaki24.