Featured
Rundunar Ƴan Sanda Ta Musanta Zargin Alaƙa Da Ƴan Bindiga a Katsina

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta musanta ikirarin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa wani bidiyo daga Jihar Katsina ya nuna jami’in dan sanda na hulɗa da ’yan bindiga. Rundunar ta ce mutanen da ke cikin bidiyon jami’an sa-kai ne da ke taimakawa wajen yaƙi da laifuffuka a jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Anietie Okokon Edem Iniedu, ya fitar, ya bayyana cewa mutanen da aka gani a bidiyon mambobi ne na ƙungiyar Vigilante Group of Nigeria (VGN) da kuma mafarauta da aka yi wa rijista, waɗanda ke aiki tare da hukumomin tsaro a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu.
Read Also: Kotu Ta Dage Shari’ar Zargin Ganduje da Almundahanar Kuɗi Zuwa Oktoba
Rundunar ta ce bidiyon ya nuna wata hulɗa ta yau da kullum tsakanin jami’in dan sanda da jami’an sa-kai yayin da suke kan hanyarsu ta gudanar da aikin tsaro. Ta kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da bayanan da ke da’awar akasin haka, tare da gargadin cewa yaɗa ƙarya da bayanan da za su iya tayar da hankalin jama’a na iya jawo hukunci a ƙarƙashin doka.