Featured
Jami’ar Northwest Kano Ta Kori Dalibai 34 Kan Laifukan Jarabawa

Jami’ar Northwest da ke Kano ta kori ɗalibai 34 tare da ɗaukar wasu matakan ladabtarwa bayan nazarin rahoton kwamitin binciken laifukan jarabawa na zangon karatu na biyu na shekarar 2024/2025.
Sanarwar da Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Abubakar Ibrahim, ya fitar ranar Talata 30 ga Yuni, 2026, ta ce an kuma dakatar da karatun ɗalibai 18, yayin da aka bai wa ɗalibai 22 gargaɗi a rubuce saboda laifukan da suka shafi jarabawa.
Read Also : Jarrabawar NECO : Ɗalibai 36 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Har Yanzu Suna Hannun Ƴan Bindiga – Rundunar Ƴansanda
Haka kuma, jami’ar ta wanke ɗaliba Rukayya Ahmad Zukuri daga zargin da ake mata, tare da tunatar da ɗalibai muhimmancin bin ƙa’idojin jarabawa da riƙon amana a harkokin karatu. Kakaki24 ta ruwaito cewa matakan sun biyo bayan amincewar mahukuntan jami’ar da rahoton kwamitin bincike.