Featured
Shugaban Karamar Hukumar Rimingado Ya Sake Biyan Kuɗin Rajistar Ɗaliban School Of Nursing Madobi a Karo Na Uku

Shugaban Karamar Hukumar Rimin Gado, Hon. Muhammad Sani Salisu Jili, ya sake biyan kuɗin rajistar ɗaliban asalin Karamar Hukumar Rimin Gado da ke karatu a School of Nursing, Madobi, a karo na uku.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin ƙaramar hukumar na ci gaba da tallafa wa harkar ilimi da bunƙasa ƙarfin matasa, musamman waɗanda ke karatun fannin kiwon lafiya, domin su samu damar kammala karatunsu ba tare da tangarɗa ba.
Read Also : Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Amurka Da Iran Ta Rushe – Donald Trump
Ɗaliban da suka amfana da wannan tallafi sun bayyana farin cikinsu tare da yabawa shugaban ƙaramar hukumar bisa irin kulawa da goyon bayan da yake bai wa ilimi da ci gaban matasan yankin.
Al’ummar Karamar Hukumar Rimin Gado sun bayyana wannan mataki a matsayin abin a yaba, tare da fatan irin wannan tallafi zai ci gaba da ƙarfafa gwiwar matasa wajen neman ilimi da hidimtawa al’umma.
RAHOTO
Arribbabatu sani yakasai
Jami ar yada labarai karamar hukumar rimin gado