Featured
Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Zargin Peter Obi Kan Barazanar Kashe Shi
Fadar Shugaban Kasa ta musanta ikirarin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, cewa gwamnatin tarayya na bibiyarsa tare da hana shi gudanar da harkokinsa. Mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce zargin ba shi da tushe balle makama.
Peter Obi ya bayyana a wata hira cewa ba zai iya tabbatar da zai rayu har zuwa zaɓen shugaban kasa na 2027 ba, yana mai zargin cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin dakile ayyukansa tare da matsa lamba kan masu hulɗa da shi.
Read Also : Dole Ne Mu Haɗa Ƙarfi da Ƙarfe Domin Magance Matsalar Tsaro a Arewacin Najeriya – Sarkin Musulmi
Sai dai Onanuga ya bayyana kalaman Obi a matsayin ƙarya da farfaganda, yana mai cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta da niyyar muzgunawa Obi. Ya ƙara da cewa gwamnati na mayar da hankali ne kan aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
