Featured
Ƙarin Kuɗin WAEC Da NECO Zai Hana Yara Dayawa Samun Damar Yin Karatu – Atiku

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki ƙarin kuɗin jarabawar WAEC da NECO zuwa Naira 50,000 daga shekarar 2027, tare da ƙarin kuɗin Makarantun Tarayya na Unity Schools. Ya bayyana matakin a matsayin rashin yin la’akari da halin ƙuncin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke ciki.
Atiku ya ce a daidai lokacin da iyalai ke fama da hauhawar farashi, tsadar abinci da sufuri da kuma ƙarancin kuɗaɗen shiga, bai kamata gwamnati ta ƙara tsadar ilimi ba. Ya yi gargaɗin cewa ƙarin kuɗaɗen zai hana yara da dama, musamman daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi, samun damar ci gaba da karatu.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya janye ƙarin kuɗin tare da kira ga gwamnatin tarayya ta ƙara zuba jari a ilimi, inganta makarantu, ɗaukar ƙarin malamai da tabbatar da cewa talauci bai hana kowane yaro ɗan Najeriya samun ilimi ba.