Featured
DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Kwace Kadarori 48 Da Ake Alaƙantawa da Abubakar Malami

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin kwace kadarori 48, ciki har da wata jami’a, da ake alaƙanta wa tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, tare da mayar da su hannun Gwamnatin Tarayya.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta ce EFCC ta gabatar da hujjojin da suka tabbatar wa kotu cewa ana zargin kadarorin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka, yayin da Malami ya kasa tabbatar da cewa ya mallake su ta hanyar da ta dace. Kotun ta kuma yi watsi da ƙorafe-ƙorafen da Malami, iyalansa da wasu kamfanoni masu alaƙa da kadarorin suka shigar.
Read Also : Majalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kafa Hukumomin KAMA da KADCA Bayan Rushe Hukumar KNUPDA
Sai dai kotun ta soke umarnin kwace wasu kadarori tara da ke jihohin Kebbi da Kaduna, bayan ta ce EFCC ba ta tabbatar da cewa an mallake su ta hanyar da ta saɓa wa doka ba. Tun da farko, hukumar ta nemi a kwace kadarori 57 da ta kiyasta darajarsu ta kai Naira biliyan 212.8.