Featured
INEC Na Duba Yiwuwar Yin Zaɓen Shugaban Ƙasa Na Gwaji
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa tana duba yiwuwar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na gwaji kafin babban zaɓen 2027, domin tantance inganci da sahihancin kayayyaki da na’urorin zaɓenta.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake karɓar baƙuncin jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr. Richard Montgomery, a hedikwatar INEC da ke Abuja. Ya ce shirin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da aka samu bayan zaɓen 2023.
Read Also : ADC Ta Bukaci Majalisa Ta Yi Bincike Kan Ingancin Lafiyar Tinubu
Farfesa Amupitan ya ce matakin na cikin ƙoƙarin hukumar na inganta fasahar gudanar da zaɓe, ciki har da tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a ta na’ura, amfani da shafin IReV wajen tura sakamakon zaɓe, da kuma ƙarfafa tsaron tsarin.
