Connect with us

Featured

Rundunar Sojin Najeriya Na Neman Wani Soja Kan Zargin Sayarwa da Ƴanbindiga Kakin Soji

Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, ta hannun sashen kula da kayan aikinta, ta ayyana neman wani jami’inta mai suna Mohammed Yusuf Amutu ruwa a jallo bisa zarginsa da sayar da kakin soji ga ƴan ta’adda da sauran masu aikata laifuka.

Sanarwar ta ce jami’in, wanda kurtu ne, ya tsere daga wurin aikinsa bayan zargin alakarsa da ƴanbindiga ta bayyana, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin gano inda yake domin kama shi da gurfanar da shi gaban hukuma.

Read Also : Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Kamfanin Jiragen Sama Mallakin Jihar

Rundunar ta jaddada cewa ba za ta lamunci rashin ɗa’a ko duk wani aiki da zai iya jefa tsaron ƙasa cikin haɗari ba, tana mai gargadin cewa duk jami’in da aka samu da laifin taimaka wa masu laifi ta irin wannan hanya zai fuskanci hukunci.

Haka kuma, rundunar ta yi kira ga al’umma da su taimaka wajen kai rahoton Mohammed Yusuf Amutu idan suka gan shi, ta hanyar sanar da sansanin soji ko wata hukuma ta tsaro mafi kusa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet