Featured
Akanta Janar Zai Gurfana Gaban Majalisa Kan Kasafin Kuɗin Hukumar Bogi

Akanta Janar na Ƙasa, Shamseldeen Ogunjimi, zai gurfana a gaban Kwamitin Wucin Gadi na Majalisar Wakilai domin amsa tambayoyi kan yadda aka ware wa wata hukumar bogi sama da naira biliyan 1.32 a cikin Kasafin Kuɗin 2026.
Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisa Yusuf Gagdi, na gudanar da bincike kan yadda aka kafa Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC), wata hukuma da Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta san da wanzuwarta ba.
Read Also : Rejoinder: “Kano First Air” Is A Vision, Not A Reward For Perfection
Ana sa ran zaman zai mayar da hankali kan yadda aka sanya kuɗaɗen hukumar cikin kasafin kuɗi, tare da gano mutanen da ke da hannu wajen shigar da wannan tanadi.
Majalisar na sa ran samun bayanai daga Akanta Janar domin fayyace yadda lamarin ya faru da kuma tabbatar da gaskiyar abin da ya jawo ware wa hukumar da ba a amince da ita ba kuɗi a kasafin shekarar 2026.