Connect with us

Featured

Sojoji Sun Kama Jami’in Da Ake Nema Ruwa A Jallo Kan Zargin Sayar Da Kayan Soji Ga Ƴan Ta’adda

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da kama jami’inta, Private Mohammed Yusuf, wanda aka ayyana nema ruwa a jallo bisa zargin hannu wajen samar da kayan soji ga ƴan ta’adda da sauran masu aikata laifuka. An kama shi ne a Maiduguri yayin da ake zargin yana ƙoƙarin tserewa zuwa Kamaru.

Rundunar ta ce dakarun Operation Hadin Kai ne suka cafke shi a tashar mota ta Jidari bayan samun sahihan bayanan sirri. Binciken farko ya nuna cewa ya tsere daga sansaninsa tun ranar 7 ga Yulin 2026, sannan ya ɓuya a unguwar Gomari Costain da ke Ƙaramar Hukumar Jere.

Read Also : Tinubu ya Gaji Ya Kamata Ya Yi Ritaya – Peter Obi 

A cewar rundunar, an ayyana neman Mohammed Yusuf ruwa a jallo tun ranar 23 ga Yulin 2026 saboda irin waɗannan zarge-zarge. Ta ce ana ci gaba da bincike domin gano cikakken irin rawar da ya taka da kuma sauran mutanen da ake zargin suna da hannu a lamarin.

Rundunar Sojin ta ce kama jami’in ya nuna tasirin ayyukan tattara bayanan sirri da jajircewarta wajen hukunta duk wani jami’i da ke aikata abin da zai kawo cikas ga ɗabi’ar aikin soja da tsaron ƙasa. Ta kuma buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet