Featured
Ƴan Bindiga Sun Kashe Kanal Ɗin Soja a Nasarawa

Wasu ’yan bindiga sun kashe wani babban jami’in soji, Kanal Abdussalam A. Ude, a lokacin da ake zargin sun kai hari domin sace shi a gidansa da ke Badna, Ƙaramar Hukumar New Karu ta Jihar Nasarawa.
Lamarin ya faru ne a daren Litinin yayin da ake ruwan sama, inda maharan suka kutsa gidan jami’in tare da ƙoƙarin yin garkuwa da shi.
Sai dai jami’in ya yi tsayin daka, kafin daga bisani su harbe shi sau da dama.
Read Also : Majalisar Wakilai Ta Bai Wa Sufeto Janar Sa’o’i 48 Ya Gabatar Da Wanda Ake Zargi Da Jagorantar Hukumar Bogi
Wani ɗan jarida da ke zaune a yankin da kuma wani shugaban al’umma sun tabbatar da faruwar lamarin. Rundunar ’yan sandan Abuja ta ce bincike ya tabbatar da cewa harin ya faru ne a Nasarawa, ba cikin Abuja ba.
Rundunar ’yan sandan FCT ta ce an tura jami’an tsaro da na leƙen asiri zuwa al’ummomin da ke iyaka da Nasarawa domin hana masu aikata laifuka kutsawa Abuja. Ta kuma bukaci kafafen yaɗa labarai da jama’a su tabbatar da bayanan tsaro kafin wallafa su.