Featured
Sojoji sun ceto Laftanar Kanal da wani farar hula da aka sace a Enugu

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto wani babban jami’in soja, Laftanar Kanal Ofor Amobi, da wani farar hula mai suna Ikechukwu Onwuanra, bayan shafe kwanaki 10 ana gudanar da aikin nemansu a Jihar Enugu.
Rundunar ta ce an ceto mutanen ne da sanyin safiyar Juma’a, bayan dakarunta sun matsa wa masu garkuwa da mutanen lamba. Sojojin Sector 1 na Operation UDO KA ne suka gudanar da aikin tare da wasu jami’an rundunar sojin ruwa da na musamman.
Read Also : Zaɓar Atiku a matsayin mataimakina shi ne babban kuskuren da na yi – Obasanjo
A cewar rahoton, dakarun sun gudanar da bincike mai zurfi a dazuzzuka da wasu al’ummomi da suka haɗa da Inyi, Awlaw da Akpugo-Eze a Ƙaramar Hukumar Oji River. Bayan samun bayanan sirri daga ’yan sanda da misalin ƙarfe 2 na dare, sojojin sun kai farmaki inda aka gano mutanen a gefen wani daji.
Rundunar ta ce mutanen biyu sun samu raunukan harbin bindiga, sannan aka garzaya da su Asibitin Kiwon Lafiya na 82 Division domin kulawa. Binciken farko ya nuna cewa an rufe musu ido, aka kai su wani wuri da ba a san inda yake ba, daga bisani aka watsar da su a wani daji da ke kan iyakar Enugu da Anambra.