Connect with us

Featured

Sau ɗaya Tinubu yake cin abinci a kullum, wani lokacin ma da ƙafa yake zuwa ofis – Shugaban NRS

Shugaban Hukumar Kula da Haraji ta Najeriya (NRS), Zacch Adedeji, ya yi watsi da zargin cewa jami’an gwamnati na yin rayuwa cikin almubazzaranci, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu ba ya rayuwa cikin almubazzaranci duk da matsayinsa.

Adedeji ya bayyana hakan ne a wata hira da Channels Television, inda ya ce Tinubu kan yi tafiya da ƙafa daga gidansa zuwa ofis, sannan yana amfani da mota ne kawai idan zai je filin jirgin sama. Ya kuma ce shugaban yana cin abinci ne sau ɗaya kacal a rana.

Read Also : Zaɓen 2027 : Ɗan takarar gwamnan Kano a ADC ya zaɓi ɗan shekara 36 a matsayin mataimakinsa

Ya ce a cikin watanni ukun da suka gabata, Tinubu bai fita daga Najeriya ba, yana mai cewa shugaban na yawan zama a ofis yana duba takardu da gudanar da ayyukansa. Adedeji ya kuma kalubalanci masu magana kan yawan motocin alfarma da ke cikin ayarin shugaban.

A cewarsa, babu laifi shugaban ƙasar ya mallaki motoci irin su Escalade, yana mai tambayar yadda hakan zai zama abin da za a kira “rayuwa cikin almubazzaranci”. Adedeji ya kuma ce bai ga shugaban yana yawan halartar bukukuwa ko zuwa hutu ba cikin shekaru ukun da suka gabata.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetjojobetcasibomcasibommatbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantgrandpashabetcasibomnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet