Featured
Gwamnatin Kano ta kawo ƙarshen rikicin Rimin zakara da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsawon shekaru

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta kawo ƙarshen taƙaddamar mallakar gonaki, filaye, kangwaye da gidaje a yankin Rimin Zakara, ta hanyar biyan diyya ga dukkan mutanen da aka tabbatar suna da haƙƙin mallakar kadarorin.
Kwamishinan Ƙasa da Tsara Birane na Jihar Kano, Hon. Abduljabbar Muhammad Umar Garko, ne ya bayyana hakan yayin bikin kammala shirin biyan diyya ga mamallakan kadarorin da taƙaddamar ta shafa a yankin.
Garko ya ce gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta kashe biliyoyin naira wajen biyan diyyar, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin al’ummomin da ke kewaye da Rimin Zakara da kuma Jami’ar Bayero Kano.
Ya ce gwamnati ta samar da cikakken tsari domin tabbatar da cewa babu wanda zai rasa haƙƙinsa a yankin, matuƙar ya bi hanyoyin da doka ta tanada wajen tabbatar da mallakar kadarorinsa.
Kwamishinan ya yaba wa Jami’ar Bayero Kano da mazauna yankin bisa haɗin kai da haƙurin da suka nuna wajen cimma matsaya. Ya jaddada cewa manufar gwamnatin jihar ita ce tabbatar da adalci, zaman lafiya da kuma kare haƙƙin dukkan waɗanda aka tabbatar da mallakarsu bisa tsarin doka.