Featured
EFCC ta kori ma’aikata sama da 40 sakamakon zargin cin hanci
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta ce ta kori ma’aikatanta sama da 40 cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata, sakamakon zarginsu da aikata cin hanci da sauran laifukan kuɗi.
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ya ce fiye da mutum biyar daga cikin waɗanda aka kora na fuskantar shari’a a kotu, yayin da ake shirya gurfanar da wasu daga cikinsu.
Read Also : Gwamnatin Kano ta kawo ƙarshen rikicin Rimin zakara da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsawon shekaru
Olukoyede ya ce hukumar ta ɗauki sabbin matakan ƙarfafa gaskiya da riƙon amana a tsakanin ma’aikatanta, yana mai jaddada cewa EFCC ba za ta iya yaƙar cin hanci yadda ya kamata ba idan jami’anta na aikata irin wannan laifi.
Haka kuma, ya bayyana cewa hukumar ta ƙwato sama da naira tiriliyan 1.23 da dala miliyan 684.48, tare da wasu kuɗaɗen ƙasashen waje, tsakanin Oktoban 2023 zuwa Yunin 2026.
