Featured
Rundunar Ƴansanda ta kama matar da ta ƴada takardar cewa Kamfanin OPay zai dakatar da ayyukansa

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, ta kama wata mata mai suna Hafsat Abubakar, mai shekaru 27, bisa zargin ƙirƙira da yaɗa takardar ƙarya, da ke nuna cewa kamfanin OPay Nigeria Limited zai dakatar da ayyukansa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Anietie Iniedu, shi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce, OPay ta shigar da ƙorafi a ranar 31 ga Agustan da ya gabata, tana neman a gudanar da bincike tare da gano waɗanda suka ƙirƙira tare da yaɗa takardar.
Read Also : Waiya charges Informations Officer’s To Step Up Fight Against Misinformation
Ya ce cibiyar yaƙi da laifukan yanar gizo ta ’yan sanda, ta yi amfani da na’urorin binciken ƙwaƙwalwar kwamfuta, wajen gano asalin takardar, inda aka gano cewa, an yaɗa ta ne daga wani shafin X mai suna @haifah_er_abba, wanda Hafsat Abubakar ke gudanarwa. Dalilin hakan yasa aka kama ta a ranar 4 ga Satumban da muke ciki.
’Yan sandan sun ce bincike na ci gaba da gudana, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci bayan kammala binciken. A baya, OPay ta musanta cewa za ta rufe ayyukanta daga 1 ga Satumba, inda ta bayyana sanarwar da aka yaɗa a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya.