Connect with us

Featured

Dawo da tallafin man fetur zai rage mana ribar da muke samu – Matatar Dangote

Matatar Man Dangote ta yi gargadin cewa sake dawo da tallafin man fetur ko sanya iyaka kan farashin mai na iya rage ribar da take samu, tare da kara wahalar hasashen kudaden shigar kamfanin. Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin takardun bayanan shirin sayar da hannayen jarinsa ga jama’a (IPO).

Dangote Refinery ta ce kudaden shigarta da ribarta suna da alaka kai tsaye da farashin da take iya sayar da man da ta tace. Kamfanin ya kuma bayyana cewa duk wani sauyi a manufofin gwamnati kan tallafin man fetur na iya yin tasiri ga harkokin kasuwancinsa.

Read Also : Majalisar Dokokin Najeriya Ta Dakatar Da Ziyarar Aiki Zuwa Afirka Ta Kudu

Kamfanin ya kara da cewa rashin tabbas game da manufofin gwamnati kan tallafin man fetur da farashin mai na iya kawo cikas ga shirye-shiryen kasuwanci da kuma hasashen kudaden shigar da yake sa ran samu.

Bayanin ya zo ne a daidai lokacin da kamfanin ke shirin fitar da hannayen jarinsa ga jama’a ta hanyar IPO.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet